Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

'Yan Afrika ta kudu na zanga-zangar kin jinin baki saboda rashin aikin yi

Dubban ‘yan Afrika ta kudu ne ke gudanar da zanga-zangar kin jinin baki yau asabar a sassan kasar inda suka yi dandazo a wata cibiyar bakin haure rike da kwalaye suna musu ihun su koma gida.

Rashin aikin yi na ci gaba da tsananta tsakanin matasan Afrika ta kudu.
Rashin aikin yi na ci gaba da tsananta tsakanin matasan Afrika ta kudu. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wasu ganau sun ce galibin masu zanga-zangar na kuka ne da hawaye tare da rokon bakin su bar musu kasa.

Zanga-zangar dai na da nasaba da yadda rashin aikin yi yakai kashi 35 tsakanin al’ummar Afrika ta kudu kashi 65 kuma tsakanin matasan kasar wanda ke da nasaba da yadda baki kan karbi aiki komi kankantarsa kuma komi rashin kudin da za a biya.

Zanga-zangar kin jinin baki ba sabon abu ba ne a Afrika ta kudu inda ko a 2019 makamanciyarta ta haddasa kisan mutane 12 baya ga kone tarin kadarori da shagunan kasuwancin bakin a Johannesburg haka zalika irin rikicin a 2015 da 2008 ya kashe mutane kusan 100 dukkaninsu baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.