Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Anyi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Majalisar Afrika ta kudu

Ma’aikatar kashe gobara a Afrika ta kudu ta sanar da shawo kan wutar da ta tashi a Majalisar kasar jiya lahadi bayan shafe sa’o’I masu yawa jami’anta na aikin kashe ta.

Ginin Majalisar Afrika ta kudu da gobara ta tashi a ciki.
Ginin Majalisar Afrika ta kudu da gobara ta tashi a ciki. AP - Jerome Delay
Talla

Da misalin karfe 5am na asubahin jiya lahadi ne gobarar ta tashi a zauren majalisar Afrika ta kudu da ke birnin Cape Town amma ba a iya nasarar shawo kanta ba sai zuwa tsakaddare, ko da ya ke har zuwa lokacin da aka yi nasarar shawo kanta ba a samu koda mutum daya daya jikkata sanadiyyar wutar ba.

Tuni mahukuntan Afrika ta kudu suka kame wani dattijo mai shekaru 49 da ake tuhuma da sanadiyyar gobarar wadda ta haddasa gagarumar asara.

Kakkin ma’aikatar kashe gobara ta Afrika ta kudu Jermaine Carelse ta ce har yanzu akwai jami’ansu 20 da ke cikin zauren majalisar bayan nasarar kashe gobarar.

Rahotanni sun ce wutar ta faro ne daga tsaffin gine-ginen majalisar wanda ke matsayin gidajen ‘yan majalisun kasar na farko gabanin sauya musu matsuguni, inda daga bisani kuma wutar ta fantsama sabbin gine-ginen da ya kunshe zauren majalisar da muhimman wurare.

Kakakin Majalisar ta Afrika ta kudu Moloto Mothapo ya bayyana cewa ilahirin muhimman gine-ginen Majalisar ciki har da zauren da ake zama ya kone kurmus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.