An gudanar da jana'izzar Desmond Tutu a Afrika ta kudu
A yau asabar ,Afrika ta kudu ta gudanar da jana’izzar karshe ga jarumin kasar,mutumen da ya yaki tsarin nuna wariyar launin fata a kasar ,Desmond Tutu.
Wallafawa ranar:
A Afrika ta kudu,'Yan uwa ,abokanin arziki,jami’an gwamnati hata Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya halarci jana’aizzar a mujami’ar Anglicane ta Saint Georges inda aka gabatar da akwatin dake dauke da mammacin da ya rasu ranar 26 ga watan Disemba na shekarar da ta shude ya na mai shekaru 90 a Duniya.
Shugaban kasar yayinda yake gabatar da jawabin sa cikin jimami,ya bayyana mammacin a matsayin jarumi da sunan sa ya zarce kan iyakokin Afrika ta kudu a gwagwarmayar da yayi tun wancan lokaci zuwa wannan.
Ya kuma taka muhimiyar rawa tareda jarumai da suka hada da Nelson Mandela,Shugaban y ace ba za su iya mantawa da irin wadanan mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu