Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu-Corona

Shugaba Ramaphosa na Afrika ta kudu ya harbu da covid-19

Fadar shugaban kasar Afrika ta kudu ta tabbatar da harbuwar Cyril Ramaphosa da cutar covid-19, ko da ya ke ta ce shugaban na cikin koshin lafiya a yanzu haka amma ya na karbar kulawar likitoci.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu. Sumaya HISHAM POOL/AFP
Talla

Sanarwar da fadar shugaban ta Afrika ta kudu ta fitar, ta ce tun a yammacin jiya lahadi ne gwaji ya tabbatar da harbuwar shugaba Cyril Ramaphosa da cutar ta covid-19 wanda ya tilasta killace shi don bashi kulawar gaggawa.

Sanarwar ta ce shugaban wanda ya karbi rigakafi tun da jimawa, ya fara rashin lafiya ne lokacin jana’izar tsohon shugaban kasar FW de Klerk a karshen mako yayinda wasu alamomin cutar suka fara nunawa wanda ya kai ga yi masa gwajin kuma sakamako ya gano ya harbu da covid-19.

Afrika ta kudu dai na ganin sabon babin cutar ta corona ne bayan bullar nau’in Omicron da ke da saurin yaduwa fiye da wadanda suka gabace ta lamarin da ya firgita al’umma yayinda gwamnati ta dauki matakin tsaurara dokoki da kuma fadada shirin rigakafi.

Sanarwar fadar ta ce shugaba Ramahosa zai ci gaba da killace kansa a birnin Cape Town yayinda mataimakinsa David Mabuza zai ja ragamar kasar zuwa mako mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.