Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Afrika ta kudu za ta fara yiwa kananan yara rigakafin Covid-19

Ma’aikatar Lafiya a Afrika ta kudu ta sanar da shirin fara bai wa kananan yara ‘yan shekaru 12 allurar rigakafin covid-19 a mako mai zuwa baya kokarin fara baiwa masu raunin garkuwa jiki rigakafin a karo na 3.

Daga mako mai zuwa Afrika ta kudu za ta fara yiwa kananan yaran rigakafin covid-19.
Daga mako mai zuwa Afrika ta kudu za ta fara yiwa kananan yaran rigakafin covid-19. AP
Talla

Kasar wadda ke da kaso mai yawa na matasa, haka zalika ita ke da rinjayen masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki da HIV ta ce kaso mai yawa na al’ummarta za su karbi rigakafin a karo na 3 saboda raunin garkuwar jiki.

Ministan lafiya Joe Phaahla ya shaidawa taron manema labarai yau juma’a cewa Afrika ta kudu ta kammala shirin fara yiwa kananun yaran ‘yan shekaru 12 zuwa 17 rigakafin daga mako mai zuwa.

Karkashin dokar yaki da corona ta Afrika ta kudu dai duk yaran da shekarunsu ya fara daga 12 zuwa sama baya bukatar sahalewar iyaye kafin karbar rigakafin cutar ta covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.