Wuta ta lakume ginin majalisar dokokin Afrika ta kudu
A Afrika ta Kudu, wata gobara ta tashi a majalisar dokokin kasar dake Cap Town,iftila’in da ya haddasa ruftawar rufin tsofuwar majalisar kasar.
Wallafawa ranar:
Ya zuwa yanzu,babu asarar rayuka,sai dai wuta ta yadu zuwa wasu gine-ginen majalisar da suka hada da gini sabuwar makjalisar dokokkin Afrika ta kudu.
Jean Pierre Smith memba ne a da’irar magajin garin Cape Town,ya sheidawa manema labarai cewa duk da ruftawar rufin tsofuwar majalisar dokkokin kasar,jami’an kwana-kwana na iya kokarin ceto abinda ya saura daga kayakin tarihi musaman littatafan dake ajiye a zauren tsofuwar majalisar dokkokin .
Shugaban kasar Cyril Ramaphosa da ya isa wurin ya sheidawa manema labarai cewa ,yan sanda na tsare da mutun daya yanzu haka,kuma bincike na tafiya a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu