Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu na bincike kan tashin gobara a babban barikin Sojinta na sama

Mahukuntan Afrika ta kudu sun fara bincike kan musabbabin gobarar da ta tashi a babban sansanin Sojin saman kasar jiya lahadi, makwanni bayan makamanciyarta a Majalisa.

Gobarar ginin Majalisar Afrika ta kudu a makon farko na sabuwars hekara.
Gobarar ginin Majalisar Afrika ta kudu a makon farko na sabuwars hekara. RODGER BOSCH AFP
Talla

Ma’aikatar tsaron Afrika ta kudu ta ce gobarar ta tashi da misalin karfe 7 na yammaci a sashen adana man fetur na sansanin sojin smaan da ke Pritoria babban birnin kasar.

Cikin lokacin da bai zarta sa’a guda ba aka yi nasarar shawo kan gobarar wadda bayanai ke cewa ba ta yi mummumar illa ba.

Sai dai sanarwar ma’aikatar tsaron ta ce bayan gano irin ta’adin da wutar ta yi ne za a bude kofar gudanar da binciken kwakwaf don dakile duk wata barazana da ka iya sake haddasa faruwar makamanciyarta a nan gaba.

A daren farko na sabuwar shekara ne makamanciyar gobarar ta kone gine-ginen Majalisar kasar da ke Johannesburg ko da ya ke akwai mutumin da ake tuhuma wanda tuni ya girbi abin da ya shuka a gaban kotu.

Shugaba Cyril Ramaphosa cikin jawabinsa kan faruwar gobarar ya ce irin abubuwan da ke faruwa a sassan Afrika ta kudu masu cike da al’ajabi na da matukar barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.