Amurka ta bukaci korar Rasha daga zama wakiliya a Hukumar kare Hakkin Bil Adama
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken ya bukaci korar Rasha daga zama wakiliya a Hukumar kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya saboda mamayar da ta yiwa Ukraine.
Wallafawa ranar:
Yayin da yake jawabi ga zaman Majalisar ta bidiyo, Blinken yace bai ga dalilin da kasar da ta mamaye wata kasa ta kuma aikata munanan laifuffukankare hakkin Bil Adama zata zauna a cikin majalisar ba.
Lokacin gudanar da wannan taro, jakadun kasashen duniya sun fice daga zauren taron lokacin da Sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fara jawabin sa.
Majalisar ta bayyana matukar damuwa dangane da mamaye Ukraine da Rasha tayi, wanda ya haifar da rasa dimbin rayuka da kuma tilastawa akalla mutane miliyan guda barin gidajen su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu