Isa ga babban shafi

Masu da’awar jihadi a Mali sun sako mutane 18 ciki har da sojoji 17 bayan shekaru uku

Gwamnatin Mali ta sanar da ceto mutane 18 ciki har da sojoji 17 bayan share tsawon shekaru uku a hannun masu da’awar jihadi a kasar, to sai dai gwamnati ba ta yi karin bayani ko a karkashin wace yarjejeniya ce aka ‘yantar da mutanen ba.

Wasu daga cikin magoya bayan dan jaridar Faransa  Dubois
Wasu daga cikin magoya bayan dan jaridar Faransa Dubois AFP - ANNIE RISEMBERG
Talla

Ibrahim Kebe, na kungiyar Faso-Kanu da ke fafutukar dawo da dimokuradiyya a kasar ta Mali, ya bayyana cewa akwai bayanai da dama da a yau jama’a ke neman sani daga mahukunta, watakila ana boye bayanan ne saboda samun nasarar ceto sauran mutanen da ke tsare a hannun masu da’awar jihadi, Jami’in y na mai cewa wannan ne ya sa ba a bayyana wa duniya ko a karkashin wadanne sharudda ne aka sako mutanen 18.

Shugaban majalisar sojin Mali Assimi Goita
Shugaban majalisar sojin Mali Assimi Goita AFP - NIPAH DENNIS

A nata bangare rundunar sojin Mali yanzu haka na rike da ‘yan ta’adda da dama a hannunta, ga alama su ne suka bayar da bayanan da suka taimaka don ceto wadannan mutane, ko kuma bangarorin biyu sun cimma yarjejeyar yin musayar fursunoni ne a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.