Majalisar Dinkin Duniya na nazari game da tsaftataccen ruwan sha a Duniya
22 ga watan Marisce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazari game da tsaftataccen ruwan sha a sassan Duniya.Bikin na bana na zuwa ne a dai dai lokacin da ake fuskantar matsalar ruwan sakamakon karancin wutar lantarki da kuma na man fetur a Najeriya, lamarin da ya sanya wasu ‘yan garuwa gudanar da yajin aiki a wani bangare a jahar Lagos.
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:53
A yan kwanakin nan karancin wutar lantarki a Najeriya ya ta’azzara matsalar karancin ruwa, lamarin da ya sa ‘yan garuwa a unguwar Idi-araba da ke birnin Lagos suka gudanar da yajin aiki kamar yadda wani magidanci Malam Habu ya tabbatar.
Asusun tallafawa ilimi, kimiyya da raya al’adu na majalisar dinkin duniya UNESCO ne ke wadannan kalamai, a wani bangare na bukukuwan Ranar ruwa ta duniya da ake gudanarwa duk ranar 22 ga watan Maris din kowacce shekara.
Ta cikin wani rahoto da ausun ta fitar, ta ce kaso 99 na dukannin narkakken abu dake karkashin kasa, ruwa ne, duk da cewa akwai karancin wannan ilimi a tsakanin al’ummar duniya.
Khamis Saleh ya kewaya birnin Lagos don gane wa idanunsa halin da ake ciki, ga kuma rahotonsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu