Majalisar sojin Burkina Faso na shirin ganawa da yan kasar a gobe
Majalisar sojin Burkina Faso a jiya asabar ta bayyana cewa ranar litinin ,gobe kenan za a soma zaman tattaunawa na kasa don tattance wa’adin ko kuma shekaru da majalisar sojin za ta share a karagar mulkin kasar kafin daga bisali ta mika mulki ga gwamnatin farrar hula.
Wallafawa ranar:
Taron da za a soma gobe litinin zai hada daukacin masu ruwa da tsaki a harakokin siyasa,kungiyoyin farraren hula,wakilan jama’a.
Ranar laraba da ta gabata ne wani kwamity na musaman da majalisar sojin ta MPSR ta kafa ,ya shawarci sojojin na ganin sun share watanni 30 a kan karagar mulkin kasar ta Burkina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu