Senegal ta shirya don kawar da kungiyar Burkina Faso a Kamaru
A yau laraba kungiyar kwallon kafar Senegal za ta fafata da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso a wasar daf da na karshe a birnin Yaounde.Wannan dai ne karo na biyar da kungiyar kwallon kafar Senegal ke kaiwa wannan mataki, yayinda Burkina Faso ke cimma wannan mataki sau hudu a tarihi.
Wallafawa ranar:
A shekara ta 2013 kungiyar kwallon kafar Burkina Faso ta kai mataki na karshe,inda kungiyar kwallon kafar Najeriya ta lallasa ta da ci 1 mai ban haushi.
Mai horar da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso Kamou Malo yayin tattaunawa da manema labarai a kasar ta Kamru ya jaddada cewa kam a wannan karo ,ya na yekini n za su fice wannan mataki zuwa wasar karshe.Babu shaka Burkina Faso za ta lashe wannan kofi.
Kazalika yan wasan Senegal na sa ran kafa tarihi a wannan karo.
Yan wasan Senegal da suka hada da Abdou Diallo dan wasan baya, Sadio Mane dan wasan gaba, ‘wannan karo kam sun shirya don ganin sun koma da wannan kofi a gida’.
Mai horar da kungiyar kwallon kafar Senegal Aliou Cisse babu shaka ,zuwan su kasar ta Kamaru da shirin lashe wannan kofi ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu