Isa ga babban shafi

ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga cikin ta sakamakon juyin mulkin

Kungiyar ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga cikin ta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, amma kuma ta jinkirta sanyawa kasar takunkumi har sai bayan ganawar da ake saran yi tsakanin shugabannin kungiyar da sojojin.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra. © Reuters
Talla

Shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo ya jagoranci taron gaggawar da akayi yau juma’a, domin tattauna batun juyin mulkin na Burkina Faso ganin yadda matsalar ke fadada a yankin Afirka ta Yamma.Taron shugabannin ya amince da shirin tura tawaga guda biyu zuwa Ouagadougou daga gobe asabar domin ganawa da sojojin da suka yi juyin mulkin wanda zai je kasar a karkashin jagorancin Babban Hafsa a kungiyar ECOWAS.

Shugabannin ECOWAS yayin bude taron su a Accra
Shugabannin ECOWAS yayin bude taron su a Accra © Nigeria presidency

Ana saran shugabannin kungiyar ECOWAS su sake gudanar da wani taro a ranar 3 ga watan Fabarariru a birnin Accra domin jin ba’asi daga wurin kwamitocin da zasu ziyarci Burkina Faso da kuma daukar mataki nag aba.

Taron shugabanin kasashen ECOWAS
Taron shugabanin kasashen ECOWAS © Nigeria presidency

Shugaban kungiyar Nana Akufo-Addo ya bayyana takaicin sa yadda sojoji ke kawar da zababbun shugabannin a yankin, inda ya bukaci daukar mataki mai karfi domin kare dimokiradiya. Addo yace dawowar juyin mulkin a yankin su, wani karan tsaye ne ga dokokin dimokiradiyar su, kuma barazanace ga zaman lafiya, tsaro da zamantakewar Afirka ta Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.