Isa ga babban shafi

Amurika na matsawa China kan taimakawa Rasha

Shugaban Amurka Joe Biden zai tattaunawa da Shugaban China Xi Jimping da nufin neman China ta kaucewa batun taimakawa Russia a wannan yaki da Rasha ke yi da Ukraine kusan kwanaki 23 da soma yakin.

Yankin Kharkiv da dakarun Rasha suka kaiwa hari
Yankin Kharkiv da dakarun Rasha suka kaiwa hari AFP - SERGEY BOBOK
Talla

A jiya alhamis kasar Amurka ta fito karrara inda ta bayyana shirin ta na sanyawa China matsin lamba don ganin ba ta goyi bayan mammayar da Rasha ke yiwa Ukraine yanzu haka.

Shugabanin kasashen biyu za su tattaunawa ta wayar talho a yau juma’a,yayinda wasu rahotanni ke nuni cewa Amurka ta nuna matukar damuwa bayan samun labarin cewa China na kokarin  taimakawa Rasha da  makamai da za a yi amfani da su a Ukraine.

Harin dakarun Rasha a filin tashi da saukar jiragen birnin Lviv, dake kasar Ukraine
Harin dakarun Rasha a filin tashi da saukar jiragen birnin Lviv, dake kasar Ukraine REUTERS - KAI PFAFFENBACH

Wannan tattaunawa tsakanin Joe Biden da Xi Jimping ,tamkar kashedi ne Amurka ke yiwa China na cewa har ta kuskura ta taimawa Rasha a wannan yaki da take da Ukraine,China  ba za ta ji da dadi ba, kamar dai yada shugaban diflomasiyar Amurka Anthony Blinken ya tseguntawa manema labarai.

Yankunan da kasar Rasha ta kama a Ukraine
Yankunan da kasar Rasha ta kama a Ukraine © Infographie FMM

Daddadiyar hulda dake tsakanin China da Rasha na fuskantar kalubale a cewar mashar’anta ganin ta yada manyan kasashen Duniya ke fatan ganin China ta juyawa Rasha baya,duk da haka China na mammaki karfi da Ukraine ke ci gaba da nunawa tun bayan barkewar wannan yaki .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.