Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasɗinu

Ƴan sandan Isra'ila sun sake ƙutsawa masallacin al-aqsa

Wata sabuwar takaddama ta sake barkewa da safiyar yau Juma'a tsakanin 'yan sandan Isra'ila da masu zanga-zangar Falesdinawa a harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

Wasu Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila suka tarwatsa a birnin Kudus.
Wasu Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila suka tarwatsa a birnin Kudus. © REUTERS/Ammar Awad
Talla

'Yan sandan Isra'ila sun kutsa harabar masallaci, yayin da matasan Falesdinawa suka yi ta jifarsu da duwatsu, lamarin da ya kai ga jikkatar wasu. A duk shekara musaman lokacin azumin Ramadana,ana fuskantar irin wannan tshin hankali tsakanin Isra’ila da  Falesdinawa dake ci gaba da neman inci daga mammayar yankunan su da Isra’ila ke cigaba da yi yanzu haka.

Yan Sandan Isra'ila yayin aikin suturi a Gaza
Yan Sandan Isra'ila yayin aikin suturi a Gaza © AFP

Rikicin baya-bayan nan tsakanin ‘yan sandan Isra’ila da Falesdinwa a masallacin na Al-Aqsa yayi sanadin jikkata sama da mutane 200 galibi Falasdinawa, matakin da haifar da tofin Allah cine daga wasu shugabannin kasashen Larabawa ga kasar Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.