An dage zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Chadi da 'yan Tawaye a Doha
A yau lahadi ya kamata a soma zaman tattaunawa a Doha dake Qatar tsakanin wakilan majalisar sojin Chadi da shugabanin yan tawaye dake dauke da makamai .
Wallafawa ranar:
Wannan zama da aka dage zuwa wani lokaci na a matsayin zakaran gwajin dafi a tsarin da majalisar sojin kasar a karkashin shugabancin Mahamat Idriss Deby Itno na kawo karshen barraka da aka share tsawon shekaru kasar na fama da shi.
Samun nasarar zaman na Doha zai taimaka matuka na ganin an cimma sulhu tsakanin bangarorin da kuma sa ran cimma nasara a taron sulhunta yan kasar ga baki daya watanni goma bayan mutuwar Idriss Deby Itno a fagen daga,wanda bayan haka ne dan sa tareda gundumuwar janar-janar guda 15 na kasar ya sabi ragamar tafiyar da kasar ta Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu