Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Amurka ta yi watsi da bukatar Rasha ta tattaunawa kan Ukraine

Amurka ta yi watsi da tayin Rasha na tattaunawa da Ukraine wanda ta kira da mai cike da shiririta yayinda ta bukaci Moscow ta gaggauta janye dakarunta daga Kyiv.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Sanarwar ma’aikatar wajen Amurkan ta ruwaito kakakinta Ned Price na cewa dole ne Rasha ta nuna dattako wajen bin tanadin diflomasiyya a rikicin da ke tsakaninta da Ukraine.

Kiran na Amurka na zuwa a dai dai lokacin da kasar tare da Tarayyar Turai ke lafta wani sabon takunkumi kan shugaba Vladimir Putin da ministan harkokin wajensa Sergei Lavrov.

Shugabancin Ukraine na ci gaba da neman taimakon kasashen yammaci da Amurka don dakile barazanar Rasha da ta afkawa sassan kasar sa'o'i 24 da suka gabata, sai dai shugaba Joe Biden ya nanata cewa Amurka ba za ta tura dakaru Ukraine a yanzu ba.

Sai dai Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar ad shirin girke dakaru a kasashen mambobinta daga gabashi don baiwa al'ummarta kariya daga Rasha.

A bangare guda cikin wani gajeren faifan bidiyo da shugaba Volodymyr Zelensky ya saki da yammacin yau ya ce bazai bar kasar ko kuma ajje mulki kamar yadda Putin ya bukata ba.

A cewar Zelensky za su zauna a Ukraine ba gudu ba ja da baya har sai sun yi nasara kan Rasha.

Zuwa yanzu mutane fiye da dubu 50 suka tsere daga Ukraine yayinda wasu 137.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.