Isa ga babban shafi
Indiya - Afghanistan

India na kwashe jami'an diflomasiyyarta a Kandahar saboda barazanar Taliban

Indiya ta kwashe kimanin jami’an diflomasiyyarta da jami’an tsaro 50 daga karamin ofishin jakadancinta da ke Kandahar, tsohuwar tingir kungiyar Taliban da ke kudancin Afghanistan, bayan an kwashe kwanaki ana gwabza fada.

Mayan sakai dake taimakawa sojin gwamnatin Afghanistan yakar Taliban, 6 ga watan Yuli 2021.
Mayan sakai dake taimakawa sojin gwamnatin Afghanistan yakar Taliban, 6 ga watan Yuli 2021. Naseer Sadeq AFP
Talla

A makon da ya gabata kungiyar na masu tayar da kayar bayan ta yi ikirarin cewa yanzu tana iko da kashi 85 na Afghanistan, kuma ta karbe yawancin su ne tun a farkon watan Mayu lokacin da sojojin kasashen waje da Amurka ke jagoranta suka fara janyewarsu ta karshe daga kasar.

'Yan Taliban din sun kuma yi artabu da sojojin gwamnati a wannan makon a gefen garin Kandahar, babban birnin lardin Kandahar, makenkesar kungiyar masu kaifin kishin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.