Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Afghanistan ta sha alwashin kwato yankunan da ke hannun Taliban

Gwamnatin Afghansitan ta sha alwashin karbe iko da yankunan da mayakan kungiyar Taliban su ke rike da su bayan fafatawar da suka yi da dakarun su a cikin wannan mako.

Dakarun Sojin Afghanistan.
Dakarun Sojin Afghanistan. via REUTERS - Afghanistan Ministry of Defence
Talla

Yanzu haka gwamnati ta tura daruruwan sojojin ta yankin arewacin kasar kwana guda bayan da akalla soji dubu guda suka tsallaka zuwa cikin Tajikistan domin samun mafaka.

Tun bayan kaddamar da shirin fara janye sojojin Amurka da NATO, Kungiyar Taliban ta zafafa hare haren da ta ke kaiwa a cikin kasar tare da kwace iko da wasu yankuna ciki har da Kandahar guda cikin manyan biranen kasar.

Amurka ta sanar da cewa dakarunta za su kammala ficewa daga kasar cikin watan Agusta mai zuwa karkashin yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ta Taliban.

Sai dai wasu na diga ayar tambaya kan yiwuwar Afghanistan ta gaza wajen fatattakar mayakan na Taliban wadanda bayanai ke cewa suna kara karfi musamman bayan tsananta hare-haren a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.