Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Mayakan Taliban sun fara mamaye muhimman yankunan Afghanistan

Al’ummar yankin Kandahar na Afhganistan sun fara tserewa daga gidajen su bayan da mayakan Taliban ke samun nasarori a yakin da suke yi da dakarun gwamnatin kasar. Ya zuwa yanzu dai Mayakan na Taliban sun fara kwace wasu yankuna masu muhimmanci a daren Lahadi.

Wasu gungun mayaka dake taimakawa sojojin Afghanistan a yaki da Taliban
Wasu gungun mayaka dake taimakawa sojojin Afghanistan a yaki da Taliban REUTERS - STRINGER
Talla

Rahotanni daga Afghanistan din na cewa Mayakan na Taliban na cigaba da matsa kaimi wajen kai hare-hare da nufin kwace yankuna masu muhimmanci daga ikon gwamnatin kasar.

Tsanantar hare-haren dai na zuwa ne tun bayan da dakarun Amurka suka soma ficewa daga kasar mai fama da rashin kwanciyar hankali.

Yankin Panjwai na daga cikin yankunan da mayakan Taliban din suka kwace a kudancin kasar kwanaki biyu kachal bayan da dakarun sojin Amurka da na Nato suka karkare ficewa daga kasar baki daya.

Garin Panjawai da ‘yan Taliban din suka kwace dai nan ne mahaifar shugaban mayakan na Taliban Hibatullah Akhundzada, yankin da ya dade yana fama da hare-hare mayakan na Taliban da nufin kwace shi.

Kandahar dai shine waje na Farko da mayakan Taliban suka fara kaddamar da hare-haren su tun bayan samar da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.