Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Harin ta'addanci ya hallaka fararen hula 11 a Afghanistan

Akalla fararen hula 11 da suka hada da mata hudu da yara kanana uku suka gamu da ajalinsu a kasar Afghanistan, lokacin da wata motar bas na safa-safa ta aukawa wani bam da aka dana a gefen hanya, a dai dai lokacin da babban mai shiga tsakani na Amurka Zalmay Khalilzad ke ziyara a Kabul.

Jami'an tsaron Afghanistan lokacin da suka ziyarci motar da ta taka nakiya a Kabul, 1 ga watan Yuni 2021
Jami'an tsaron Afghanistan lokacin da suka ziyarci motar da ta taka nakiya a Kabul, 1 ga watan Yuni 2021 AP - Rahmat Gul
Talla

Hari na baya-bayan nan da ya rutsa da motocin fasinja ya faru ne a yammacin Asabar a lardin Badghis da ke yammacin kasar, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar sabon rikici a watannin da ke tafe yayin da Amurka ke ci gaba da janye sauran dakarunta da suka rage a kasar.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin fashewar amma gwamnan Badghis Hessamuddin Shams ya zargi Taliban da dana bam din.

Wani jami'in lardin, Khodadad Tayeb, ya tabbatar da adadin kuma ya ce motar bas din ta fada cikin kwari bayan da bam din ya tashi da ita.

Harin na ranar Asabar ya zo ne bayan wasu fashe-fashen da aka auna kan motocin fasinja a Kabul a wannan makon, biyu daga cikinsu a ranar Alhamis a yankunan da galibin 'yan Shi'ar Hazara suka fi yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.