Isa ga babban shafi
Afghanistan-Ta'addanci

Fashewar bam a masallaci ya yi sanadin mutuwar mutane 12 a Afghanistan

Wani harin masallaci a kasar Afghanistan yayi sanadiyyar mutuwar masallata 12 kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka bayyana, wanda hakan ya kawo karshen kwanaki ukun da kungiyar Taliban ta bayar na tsagaita wuta don bukukuwan sallah karama.

Hoton cikin masallacin da ke wajen birnin Kabul na Afghanistan inda bam ya tashi har ya kashe mutane 12 a ranar Juma'a 12 ga watan Mayu.
Hoton cikin masallacin da ke wajen birnin Kabul na Afghanistan inda bam ya tashi har ya kashe mutane 12 a ranar Juma'a 12 ga watan Mayu. © AP - Rahmat Gul
Talla

Cikin mutane biyun da suka mutu har da limamin masallacin, a yayin da 15 suka jikkata.

Da take jawabi jami’ar yada labaran rundunar ‘yan sandan yankin Shakar Darah, Ferdaws Framurz ta ce 'yan ta’addan sun kai harin bam ne cikin masllacin a daidai lokacin da ake tsaka da sallah.

Wannan hari dai shine na farko tun bayan da Mayakan Taliban suka bada sanarwar tagaita wuta ta kwanaki Uku saboda bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan Sallah karama cikin kwanciyar hankali.

Dama dai kasar Afghanistan ta dade tana fama da rashin tsaro, amma abin ya kara tsananta ne bayan da Amurka ta fara janye dakarun ta daga kasar tun ranar daya ga watan da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.