Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban ta kori sojojin Afghanistan zuwa Tajikistan

Hukumomi a Tajikistan sun ce, sojojin Afghanistan sama da dubu 1 suka tsere zuwa kasar bayan sun yi artabu da mayakan Taliban.

Taliban ta zafafa hare-harenta kan sojojin Afghanistan
Taliban ta zafafa hare-harenta kan sojojin Afghanistan via REUTERS - Afghanistan Ministry of Defence
Talla

Sanarwar da masu tsaron iyakar Tajikistan suka fitar, ta tabbatar da cewa sojojin da ke aiki akan iyakar kasar da ta raba Tajikistan din da Afghanistan, sun bar wurin ne domin tsira da ransu.

A ‘yan makonnin da suka gabata rikici ya kara tsananta a Afghanistan kuma kungiyar Taliban tana samun gagarumar nasara, musamman a arewacin kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da kasashen Amurka, Birtaniya da sauran kasashen kawance suka janye dakarunsu bayan shekaru 20.

Mafi yawan ragowar sojojin kasashen waje a Afghanistan sun fice daga kasar gabanin wa’adin watan Satumba, kuma bayanai na cewa akwai damuwar cewa, sojojin Afghanistan wadanda ya kamata su karbe ikon tsaro a kasar, za su fuskanci tarin kalubale.

A karkashin wata yarjejeniya da aka kulla da Taliban, Amurka da kawayenta na kungiyar tsaro ta NATO sun amince da janye dakarunsu sakamakon amincewar da mayakan suka yi na kin bai wa kowacce irin kungiyar masu da’awa jihadi aiki a yankunan da suke iko da su.

Amma Taliban ta nuna rashin amincewarta na dakatar da yaki da sojojin Afghanistan, kuma yanzu haka rahotanni na cewa mayakan sun karbe ikon kusan kashi daya cikin uku na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.