Isa ga babban shafi
Nepal-Faransa

An gano gawar Faransawa 3 masu hawa tsauni da suka bace a Nepal

‘Yan sanda a Nepal sun ce an samu gawarwakin wasu Faransawa 3 masu hawa tsauni da suka bace a yankin tsaunukan Himalaya, kusa da inda suka bace cikin watan da ya gabata.

Yankin da Faransawa 3 suka bace a Nepal.
Yankin da Faransawa 3 suka bace a Nepal. Lakpa SHERPA AFP
Talla

Tawagar Faransawan 3 na kokarin tsallakawa tsaunin Mingbo Eiger, mai tsawon mita dubu 6, kusa da tsaunin Everest, kuma ji na karshe da aka yi musu shi ne a ranar 26 ga watan Oktoba, ta wayar tauraron dan adam.

Mummunan yanayi ya kawo cikas wajen aikin lalubo mutanen, kuma a makon da ya gabata masu aikin ceton suka ce mai yiwuwa mutanen na binne cikin dusar tarin kankara da tsawonsa ya kai bene mai hawa 5.

Wani babban jami’i a ofishin ‘yan sanda na gundumar Solukhumbu, Rishi Raj Dhakal, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa jirgi mai saukar ungulu ya dauki gawarwakin mutanen zuwa Lukla wani karamin kauye, kusa da hanyar zuwa tsaunin Everest.

Matasa 3, masu hawan tsauni, Thomas Arfi, Louis Pachoud da Gabriel Miloche na daga cikin wata tawaga da ta rabu biyu, da zummar hawa kololuwar tsaunuka dabam dabam a yankin.

Masu hawa tsaunuka sun fara komawa Nepal, bayan da annobar corono ta tilasta rufe bangaren da ke kula da sabgarsu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya daidaita tattalin arzikin kasar da ta dogara ga yawon bude ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.