Isa ga babban shafi
FARANSA-KORONA

Firaministan Faransa Jean Castex ya harbu da cutar korona

Hukumomin Faransa sun ce Firaministan kasar Jean Castex ya kamu da cutar korona, saboda haka zai killace kan sa na kwanaki 10 inda zai dinga gudanar da ayyukan sa daga gida.

Firaministan Faransa Jean Castex lokacin da ya ziyarci Belgium jiya litinin
Firaministan Faransa Jean Castex lokacin da ya ziyarci Belgium jiya litinin JOHN THYS AFP
Talla

Rahotanni sun ce Castex yayi gwaji ne sakamakon gano daya daga cikin ‘yayan sa ta harbu da cutar, abinda ya kuma tabbatar da cewar shima ya harbu.

Wannan ya sa Firaministan Belgium Alexander De Croo da ministocin sa guda 4 killace kan su, saboda ganawar da suka yi da Castex jiya litinin, lokacin da ya ziyarci kasar.

Daga cikin wadanda suka raka Castex Belgium akwai ministan cikin gida Gerard Darmanin da ministar dake kula da kasashen Turai Clement Beaune.

Firaministan mai shekaru 56 ya karbi allurar rigakafin kamuwa da cutar har sau biyu a watannin da suka gabata, kuma bai taba kamuwa da cutar bak afin wannan lokaci.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da uwargidan sa Brigitte sun harbu da cutar a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.