Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Faransa ta tura jami'an tsaro don magance tarzomar Korona

Mahukunta a Faransa sun tura karin jami’an tsaro zuwa yankin Guadelouope, bayan da aka share tsawon kwanaki ana tarzoma tare da kone-kone don nuna rashin amincewa da sabbin matakan hana yaduwar cutar Covid-19.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron BENOIT TESSIER POOL/AFP
Talla

To sai dai duk da wannan tarzoma, shugaba Emmanuel Macron ya ce ba gudu ba ja da baya, za a ci gaba da daukar tsauraran  matakai don kare lafiyar jama’a.

Ina godiya ga mazauna yankin Guadeloupe wadanda suka amince aka yi masu allurar kariya, domin idan aka yi la’akari da adadin wadanda suka karbi allurar, hakan na nuni da cewa mutane kalilan ne ke adaewa da matakan muke dauka. inji Macron.

Shugaban ya kara da cewa "mazauna yankin Guadeloupe, da yankin Martinique har ma da Guiana maza da mata duk sun fahinci cewa yin allurar abu ne da ya dace."

Macron ya ce, ba za su taba yin wasa da duk wani lamari da ya shafi kare lafiyar Faransawa ba don cimma muradunsu, yana mai cewa, za su ci gaba amfani da hanyoyin lalama don kwantar da hankulan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.