Isa ga babban shafi
Taiwan-Amurka

Amurka ta fifita Taiwan kan Rasha da China wajen gayyatar taron Demokradiyya

Shugaba Joe Biden na Amurka ya gayyaci Taiwan halartar babban taron demokradiyya da Amurka za ta karbi bakonci ta bidiyon na’ura, matakin da zai iya harzuka China wadda ba ta cikin kasashe 110 da za su halarci taron.

Shugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen na ci gaba da kokarin karfafa alakarta da kasashen yammaci don kalubalantar uwar gijiyarta China.
Shugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen na ci gaba da kokarin karfafa alakarta da kasashen yammaci don kalubalantar uwar gijiyarta China. AP - Chiang Ying-ying
Talla

Taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 9 zuwa 10 ga watan disamba shi ne irinsa karon farko da zai sake fayyace manufar Biden ta ketare game da tabbatar da bin dokokin demokradiyya.

Haka zalika taron na zuwa dai dai lokacin da rikici tsakanin Amurka da China ke ci gaba da zafafa game da yankin na Taiwan mai kwarya-kwaryar ‘yanci, bayan da yankin a baya-bayan ya ke kokarin samun goyon bayan Washington duk da kasancewarsa wani bangare na Beijing.

Cikin jerin kasashen da Amurka ta tsara gayyata zuwa taron na watan Disamba ta tsame sunan manyan abokanan gabarta wato China da Rasha.

Matakin na Amurka dai da yiwuwar y arura tankiyar da ke tsakanin China da yankin na Taiwan wanda ke kamanta tsarin demokradiyya.

China na kalubalantar duk wani yunkurin kasashen Duniya wajen kokarin baiwa Taiwan darajar kasa bisa ga kafa hujja da cewa har yanzu tana ci gaba da kasancewa wani bangare nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.