Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

WHO ta roki kasashe su sassauta matakan yaki da nau'in Omicron

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci kasashe su kwantar da hankula tare da daukar matakai masu ma’ana a kokarin yaki da sabon nau’in corona na Omicron dai dai lokacin da EU ke cewa za a iya samar da rigakafin nau’in nan da watanni 4 matukar akwai bukata.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. © Laurent Gillieron/Keystone via AP
Talla

A kiraye-kirayen da WHO ke ci gaba da yi tun bayan bullar sabon nau’in na Omicron, hukumar ta ja hankalin kasashe game da sanya dokar kulle ko tsananta dokokin han walwala dama haramta tafiye tafiye wadanda ta ce duk basu za su hana nau’in yaduwa duba da yadda zubinsa ken una saurin yaduwarsa fiye da nau’ikan da aka gani a baya.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus yayin jawabinsa ya ce ko shakka babu abin fahimta ne yadda kasashe ke kokarin kare al’ummominsu daga barazanar nau’in na Omicron wadda har zuwa yanzu ba a kai ga gano zubinta ba, yana mai cewa makamantan matakan da aka dauka a baya baza su taimaka a wannan lokaci ba.

Kalaman na Tedros Adhanom na zuwa a dai dai lokacin da hukumar kula da magunguna ta tarayyar Turai ke ganin za a iya samar da rigakafin nau’in na Omicron nan da watanni 4 matukar akwai bukatar hakan.

A bangare guda tuni Jamus ta goyi bayan shirin tilastawa mutane karbar rigakafi a wani yunkuri na ganin an shiryawa tunkarar sabon nau’in na Omicron.

Yanzu haka dai kamfanonin samar da rigakafin covid-19 da suka kunshi Modern ana Amurka da Pfizer na bincike kan rigakafin da zai yaki sabon nau’in na Omicron ko da ya ke WHO ta ce zai iya daukar makwanni gabannin kammala nazartar sabon nau’in wanda ke da saurin yaduwa fiye da wadanda suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.