Isa ga babban shafi
MATSALOLIN-JINKAI

Mutane miliyan 247 za su bukaci tallafin jinkai a shekarar 2022- MDD

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewar bukatar agaji zai karu sosai a duniya a shekara mai zuwa sakamakon yadda annobar korona ke karuwa da matsalar sauyin yanayi da kuma rikice rikicen dake jefa jama’a cikin tsananin yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanr miliyan 247 ne za su bukaci dauki a 2022.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanr miliyan 247 ne za su bukaci dauki a 2022. ASSOCIATED PRESS - Adel Hana
Talla

Hukumar jinkai ta Majalisar OCHA tayi kiyasin cewar akalla mutane miliyan 247 a duniya zasu bukaci taimako gaggawa a shekarar 2022, adadin da ya zarce na wannan shekarar da kashi 17.

Wannan adadi ya nuna cewar a cikin ko wadanne mutane 29 dake duniya, mutum guda zai bukaci agaji a shekara mai zuwa, adadin da ya zarce na shekarar 2015 da kashi 250.

Shugaban hukumar jinkan Martin Griffiths yace ba’a taba samun yawan mutanen dake bukatar agajin da ya kai na wannan lokaci ba, kuma samar musu da agajin ba’a abu ne mai dorewa ba, amma kuma ya zama dole ayi.

Gidauniyar taimakawa mabukatar ta Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin agaji sun ce ana bukatar Dala biliyan 41 domin tallafawa mutane miliyan 183 a kasashen duniya 63 a shekarar mai zuwa, adadin da ya zarce Dala biliyan 35 da aka bukata a cikin wannan shekara ta 2021.

Rahotan ya bayyana matukar damuwa akan tashe tashen hankulan da ake gani a kasashen Afghanistan da Habasha da kuma Myanmar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.