Isa ga babban shafi
Amurka-Guguwa

Kakkarfar guguwar Tornadoes ta kashe mutane 94 a Amurka

Jami’an agaji na ci gaga da aikin ceto domin gano wadanda ke da sauran numfashi bayan da mahaukaciyar guguwa da aka yiwa lakabi da Tornadoes ta afkawa jihohi 6 tare da haddasa asarar rayukan akalla mutane 94 a kasar Amurka.

Wani yanki da guguwar Tornadoes ta yiwa barna a Amurka.
Wani yanki da guguwar Tornadoes ta yiwa barna a Amurka. © AP - Mark Humphrey
Talla

Joe Biden ya bayyana guguwar a matsayin daya daga cikin iftila’I mafi muni da aka taba gani a tarihin  kasar ta Amurka, inda tuni ya tura shugaba hukumar agajin gaggauwa na tarayya zuwa Kentucky domin jagorantar aikin tattara bayanai dangane da illolin da guguwar ta haddasa.

A jihar ta Kentucky kawai guguwar ta kasshe mutane 80 a cewar gwamna Andy Beshear, baya ga lalata dimbin gidaje da masana’antu musamman a garin Mayfield, yayin da guguwar ta kashe wasu mutanen 6 a Edwardsville da ke kudancin jihar Illinois.

Guguwar ta kashe wasu haddasa asarar rayukan mutane 4 a Tennesse,  mutane 2 Arkansar sannan ta hallaka wasu mutanen 2 a Missouri kafin isarta a jihar Mississipi, lamarin da ya sa ake fargabar cewar adadin wadanda suka rasa rayukansu zai iya zarta dari daya.

Jami’an agaji wadanda ke amfani da karnuka da kuma manyan motaci da  ke daga gine-gine, sun ce har yanzu ana ci gaba da gano mutanen da ke rayukansu a karkashin tarkacen gine-gine da kuma motocin da guguwa ta share, yayin da aka samu katsewar wutar lantarki da kuma toshowar hanyoyin mota a wadannan jihohi 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.