Isa ga babban shafi

Kotun Belarus ta daure Shugaban 'yan adawa shekaru 18 a gidan yari

Wata Kotu a kasar Belarus ta zartas da hukuncin daurin shekaru 18 a kan shugaban 'yan adawar kasar Sergei Tikhanovsky saboda shirya zanga zangar adawa da shugaba Alexander Lukashenko.

Wasu daga cikin magoya bayan jagoran 'yan adawa a Belarus
Wasu daga cikin magoya bayan jagoran 'yan adawa a Belarus - AFP/File
Talla

A shekarar da ta gabata Tikhanovsky ya kaddamar da shirin takarar zabe domin kalubalantar shugaba Lukashenko amma sai gwamnati ta kama shi.

Wannan ya sa matar sa tsayawa takara a zaben da aka bayyana Lukashenko a matsayin wanda ya lashe.

Marido da principal opositora em Belarus condenado a 18 de prisão.
Marido da principal opositora em Belarus condenado a 18 de prisão. via REUTERS - BELTA

Shugaba Lukashenko da ake zargi a nahiyar Turai a matsayin shugaban kama karya ya gamu da fushin kasashendake Yankin saboda yadda yake tirsasawa 'Yan adawa abinda ya kaiga tserewar 'yan karar shugaban kasar, yayin da kasashen duniya suka ki amincewa da sakamakon zaben da aka bayyana cewar shine ya lashe.

Yanzu haka kungiyar EU da wasu kasashen Turai da Amurka sun kakabawa Belarus takunkumin karya tattalin arziki, yayin da wadda tayi karar shugaban kasa da shi ke bayyana kan ta a matsayin halartacciyar shugaban da aka zaba.

Wasu daga cikin 'yan aadawa a Belarus
Wasu daga cikin 'yan aadawa a Belarus Wojtek RADWANSKI AFP/File

Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda ko goyawa Lukashenko baya yayi tayin shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.