Isa ga babban shafi
ANNOBAR-KORONA

Korona ta kashe mutane dubu 800 a Amurka

Adadin mutanen da cutar korona ta kashe a kasar Amurka ya zarce dubu 800, wanda shine adadi mafi yawa da wata kasa ta gani dangane da wannan annobar.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden Brendan Smialowski AFP
Talla

Wannan adadi na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta bayyana samun yawan mutanen da suka harbu da cutar a Amurka ya kai miliyan 50 tun bayan barkewar ta watan Disambar shekarar 2019.

Hukumomin Amurka sun ce akasarin wadanda suka mutu sun fito ne daga cikin wadanda basu karbi allurar rigakafi ba da kuma masu yawan shekaru, yayin da alkaluma suka nuna cewar mutanen da suka mutu a wannan shekara ta 2021 sun zarce wadanda suka mutu bara.

Hukumar Lafiya tace sabon nau'in Omicron na yaduwa kamar wutar daji
Hukumar Lafiya tace sabon nau'in Omicron na yaduwa kamar wutar daji Jack TAYLOR AFP/File

Jami’ar Johns Hopkins dake sanya ido akan yaduwar cutar da kuma illar da take yi a cikin kasar tace an samu lokacin da mutane sama da 100,000 suka mutu a kasar a cikin watanni 11 kacal na wannan shekara.

'Yan majalisar dokokin Amurka sun rike fitilar kyandir cikin dare domin nuna alhini da kuma juyayin mutane sama da dubu 800 da suka rasa rayukan su a kasar.

Hukumar Lafiya ta duniya tayi gargadin cewar sabon nau'in cutar koronan da aka yiwa lakabi da Omicron na yaduwa kamar wutar daji a kasashen duniya, inda yanzu haka aka tabbatar da ita a kasashe 77.

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus yace duk yake babu tabbacin samun ta a wasu kasashe amma suna da yakinin cewar sabon nau'in ya shiga kowacce kasa ta duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.