Yawan wadanda suka kamu da Korona ya zarce mutane miliyan 75 a Turai
Yawan wadanda suka kamu da cutar Korona a Turai ya zarce mutane miliyan 75, a daidai lokacin da hukumomin kasashen nahiyar ke daukar matakan dakile yaduwar sabon nau’in cutar na Omicron, lamarin dake neman zama kadangaren bakin tulu ga jami’an lafiya.
Wallafawa ranar:
Sai dai a Birtaniya, rahoton da hukumar kididdigar kasar ta fitar ya nuna cewa an samu karin yaduwar Korona a sassan kasar, sai dai nau’in cutar an Delta ne yayi tasiri wajen hakan sabanin sabon nau’in Omicron da ya bayyana daga Afirka ta Kudu a karshen watan Nuwamban da ya gabata.
A kasar Rasha kuwa, adadin wadanda suka mutu a dalilin annobar ta Korona ya kai a kalla dubu 578 da 20, adadi mafi muni na uku a duniya.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, an gano sabon nau'in cutar a cikin kasashe 38, kari daga adadin kasashe 23 cikin kwanaki biyu kacal da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu