Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

An bada shawarar sake yin rigakafi a Faransa

Kwamitocin da aka kafa don bada shawara ga gwamnatin Faransa game da yadda take tafiyar da shirin yaki da cutar Covid-19 sun ba da shawarar sake yin allurar rigakafin cutar karo na uku.

Yadda ake tsira allurar rigakafin Korona
Yadda ake tsira allurar rigakafin Korona THOMAS KIENZLE AFP/File
Talla

A halin yanzu Faransa tana bada tallafi ne kawai ga mutanen da suka haura shekara 65 ko kuma masu fama da yanayi na yau da kullun wanda ke sa su kamuwa da kwayar cutar, da kuma ma'aikatan kiwon lafiya.

Bayanai daga hukumomin kasar sun ce daga ranar 1 ga Disamba, za a fadada shirin zuwa kan mutanen da shekarunsu suka haura 50.

Wata sanarwa da Majalisar Kula da Allurar Rigakafi, wanda masanin rigakafi Alain Fischer ke jagoranta ya bada shawarar fitar da karin rigakafin ga kowa domin tasirin matakan da zai bada damar shawo kan cutar.

Kwamitin, wanda kwararre kan cututtuka masu yaduwa, Jean-Francois Delfraissy ke jagoranta, shi ma dai ya goyi bayan shawarar a cikin wani bayanin da hukumomin da abun ya shafa suka fitar.

Shawarwarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai da dama da tsibirin Caribbean na Faransa ke kokarin kwantar da tarzoma kan dokokin da aka kafa da nufin dakile barazanar da ke sake kunnowa wanda ake kallon wani sabon babin kamuwa da cutar ne da ke saurian yaduwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.