Turai na tunanin tilasta wa al'umarta karbar rigakafin Korona
Shugabar Kungiyar Kasashen Turai Ursula von der Leyen ta ce lokaci ya yi da za su yi tunanin tilastawa jama’ar dake yankin karbar maganin rigakafin cutar korona, ganin yadda nau’in Omicron ke saurin yaduwa kamar wutar daji.
Wallafawa ranar:
Ganin yadda wasu kasashe suka fara daukar matakai daban daban na dakile cutar, von der Leyen tace duk da yake gwamnatoci ne ke da hurumin tilasta karbar rigakafin, lokaci yayi da ya dace ayi tunani akai.
Tuni Austria ta ce za ta tilasta wa kowa karbar rigakafin nan da watan Fabarariru mai zuwa, yayin da Jamus ke tunani akai.
Karuwar masu kamuwa da cutar covid-19 ya sa wasu gwamnatoci a nahiyar Turai suka maido da dokar tilasta sanya mayanin fuska, matakan bayar da tazara da kuma talaita zirga-zirga a kokarin da suke na rage yaduwar cutar, a yayin da masu sana’o’i ke fargabar samun maimaicin abin da ya faru a lokacin Kiristimeti na shekarar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu