Isa ga babban shafi

Hukumar kiwon lafiya ta yi kashedi ga kasashen Duniya dangane da cutar Korona

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargadin a cewa kada kasashe su yi gaggawar ayyana nasara kan annobar korona dakatar da yaki da bazuwar cutar.

Hukumar kiwon lafiya ta Duniya na kira ga kasashen Duniya dangane da cutar Korona
Hukumar kiwon lafiya ta Duniya na kira ga kasashen Duniya dangane da cutar Korona Thibaud MORITZ AFP
Talla

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai cewa cutar na nan daram, kuma tana dauke da hadari.

Tedros Adhanom Ghebreyesus Shugaban hukumar kiwon lafiya ta Duniya
Tedros Adhanom Ghebreyesus Shugaban hukumar kiwon lafiya ta Duniya Fabrice Coffrini AFP/Archivos

Kalaman nasa sun zo ne yayin da Danmark a ranar talata ta zama kasa ta farko daga tarrayar Turai da ta dauki matakin dage dukkanin dokokkin hana yaduwar cutar dake takaita walwala, duk da barazanar da sabon nau’in cutar omicron ke yi, yayin da wasu kasashe ke duba yiyuwar daukar makamacin wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.