WHO ta yi gargadi a kan dokar takaita zirga-zirga saboda sabon nau'in Covid
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi a game da kakaba dokar kulle sakamakon bullar sabon nau’in cutar Covid-19 na B.1.1.529, tana mai cewa zai dau makonni kafin a fahimci tasirinsa.
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiyar ta duniya ta ce kwamitin kwararrunta a kan asalin kwayoyin cutar virus na gudanar da wani taro don tattauna sabon nau’in cutar da aka fara ganowa ta wajen bincike a Afirka ta Kudu.
A yayin da kasashen nahiyar Turai suka fara haramta wa jirgen da ke tashi daga Afrika ta Kudu sauka a yankunansu, hukumar ta ce kamata ya yi kasashe su dauki matakai na kimiyya wajen yin nazarin takaita zirga zirga.
A wani taron manema labarai a Geneva, kakakin hukumar lafiya ta duniya Christian Lindmeier ya ce hukumar tana bibiyar sabon nau’in Covid-19 na B.1.1.529 da aka bada rahoton bullarsa kwanan nan, inda ya ce an gano cewa nau’in cutar na yawan canza fasali, kuma akwai bukatar a ci gaba da nazari.
A juma’ar nan Jamus da Italiya suka bi sahun Birtaniya da sauran kasashen nahiyar Turai wajen haramta wa jiragen da ke tasowa daga Afrika ta Kudu sauka a kasashen su, a yayin da gwamnatoci ke kokarin dakile yaduwar sabon nau’in Covid-19 da aka gano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu