Rigakafin Covid-19 ya rage karfin yaduwarta da kashi 40 - WHO
Rigakafin cutar Korona ya rage karfin yaduwar ta da kashi 40 cikin 100, a cewar Hukumar lafiya ta duniya ranar Laraba, tana mai gargadin cewa mutane su kiyayi abin da zai jefa su cikin hatsarin kamuwa da ita.
Wallafawa ranar:
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesu ya bukaci mutanen da aka yiwa allurar Rigakafin da su ci gaba da daukar matakan kauce wa kamuwa da cutar Covid-19 da kuma yada ta
Tedros ya lura da cewa a makon da ya gabata, fiye da kashi 60% daga cikin 100% na daukacin rahotannin da aka yada kan mace macen da ake samu yanzu, a sanadiyar cutar ta Korona yafi karfi a kasashen Turai
Shugaban ya ci gaba da cewa, karuwar adadin da aka samu a wannan karon baya rasa nasaba da karancin matsin lamba, kan tsarin kiwon lafiya da kuma gajiyawar ma’aikatan wannan bangaren.
Ya kara da cewar duk wanda ya yi allurar rigakafin yana da kariya daga kamuwa da cutar ta Korona, amma wannan ba zai hana shi kiyaye wa daga sakaci da ka iya sanya wa a kamu da ita ba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu