Isa ga babban shafi
G20 - Coronavirus

WHO ta roki kungiyar G20 ta taimakawa kasashe matalauta da rigakafin Korona

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya bukaci shugabannin kasashen G20 da su taimawa wajen ganin an wadata kasashe matalauta da maganin rigakafin cutar Korona.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya. AP - Denis Balibouse
Talla

Yayin da yake jawabi ga shugabannin dake gudanar da taron su a birnin Rome, Tedros yace daga taron da kungiyar ta gudanar bara, an baiwa mutane rigakafin cutar korona allura biliyan 7 amma abin takaici nahiyar Afirka bata samu kashi guda daga cikin maganin ba, yayin da kasashen G20 suka samu sama da kashi 80 na maganin.

Shugaban Hukumar Lafiyar yace sun fahimci nauyin dake kan kowacce gwamnati na kare lafiyar jama’ar ta, amma bukatar ganin an samu daidaito wajen raba maganin zai taimakawa kowacce kasa.

Shugaban kasashen G20 a birnin Rome na kasar Italiya.
Shugaban kasashen G20 a birnin Rome na kasar Italiya. Erin SCHAFF POOL/AFP

Tedros ya yabawa kungiyar wajen yadda take taimakawa Hukumar cimma kudirin ta na yiwa kashi 40 na mutanen duniya rigakafi nan da karshen wannan shekara, da kuma kashi 70 nan da tsakiyar shekarar 2022, yayin da ya koka akan cewar kasashe 82 na fuskantar barazanar gazawa wajen baiwa jama’ar su rigakafin saboda karancin sa.

Shugaban Hukumar ya bukaci kasashen da suka yiwa kasha 40 na mutanen su rigakafin da su taimaka wajen kara yawan taimakon maganin rigakafin da ake sanyawa cikin shirin COVAX da AVAT wanda ake baiwa kasashe matalauta.

Tedros ya kuma bukaci kasashen G20 da su taimaka wajen samar da cibiyoyin sarrafa maganin rigakafin a nahiyar Afirka, yayin da ya bayyana cewar suna bukatar akalla Dala biliyan 23 da rabi a cikin watanni 12 masu zuwa domin taimakawa kasashe da na’urorin gwaji da maganin rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.