Isa ga babban shafi
Rasha-Belarus

Rasha ta fara atisayen Sojin hadin gwiwa tsakaninta da Belarus

Rasha ta fara wani atisayen Sojin hadin gwiwa da Belarus yau alhamis matakin da ke kokarin sake dagula rikicin da ke tsakanin kasar da takwarorinta na yammaci dai dai lokacin da kungiyar tsaro ta NATO ke kokarin katange Ukraine daga mamayar Moscow.

Dakarun Rasha dubu 30 sun shiga atisayen hadin gwiwa a Belarus.
Dakarun Rasha dubu 30 sun shiga atisayen hadin gwiwa a Belarus. © AP
Talla

Atisayen wanda ake sa ran ya kai har nan da 20 ga watan Fabarairun da muke, shi ne mataki na baya-bayan nan da Rasha ta dauka wanda ya tunzura  kasashen yammaci wadanda tuni suka fara sukar matakin.

Bayanai sun ce dakarun Rasha akalla dubu 30 sun isa Belarus yau alhamis don fara atisayen Sojin na hadin gwiwa.

Sai dai har zuwa yanzu daga Moscow har Minsk basu sanar da adadin dakrun da ke cikin atisayen na Soji ba, inda Kremlin ta sanar da cewa dakarun na ta za su koma gida bayan kammala atisayen na kankanin wa’adi.

Kasashen yammacin dai na ci gaba da gargadin Rasha game da yunkurin yiwa Ukraine mamaya dai dai lokacin da dakarunta fiye da dubu 100 ke ci gaba da zama a kan iyakarta da Kiev.

Acewar ma’aikatar tsaron Amurka aikewa da dakaru dubu 30 da Rasha ta yi zuwa Belarus wani akrin barazana ne ga tsaron kasashen gabashin Turai musamman Ukraine da ke gab da fuskantar mamaya.

Acewar shugaba Volodymyr Zelensky girke dakarun a Belarus wani karin matsin lamba ne da ya tayar musu da hankali ko da ya ke yayi ikirarin cewa suna da wadatattun dakarun da za su iya baiwa kasarsu kariya daga makiyanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.