Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Gwajin makamin da Rasha ta yi ya zafafa jita-jitar yiwuwar ta mamaye Ukraine

Gwajin makamai masu linzami da dakarun Rasha suka gudanar da safiyar yau asabar ya sake tayar da hankalin kasashen yammaci inda Amurka ke ganin Moscow na nuni ne da yiwuwar mamaye Ukraine nan da ‘yan kwanaki masu zuwa ko da ya ke ta gargade ta kan hadarin da ke tattare da yin hakan.

Gwajin makamin da Rasha ta gudanar yayin atisayen hadin gwiwa da Belarus.
Gwajin makamin da Rasha ta gudanar yayin atisayen hadin gwiwa da Belarus. AP
Talla

Gidajen talabijin din Rasha sun haska wani bidiyo da ke nuna shugaba Vladimir Putin tare da takwaransa na Belarus Alexandre Lukashenko a fadar Kremlin suna kallon yadda kwamandodjin sojon ke gwajin makamin ta bidiyo.

A cewar shugaba Joe Biden Rashan na gab da mamayar Ukraine a wani yanayi da zai baiwa Duniya mamaki yayinda Kamala Harris ke cewa kasar za ta girbi abin da ta shuka matukar ya tabbata ta yi yunkurin yiwa Ukraine mamaya yayinda EU ke gargadin Putin kan fuskantar matsanantan takunkumai.

Shugaba Putin dai ya sake musanta shirin mamayar makwabciyar tasa wadda ta fusata shi kan yunkurinta na zama mamba a NATO da kuma kokarin sake kusanci da kungiyar EU wadanda ke matsayin abokanan gabar Rasha.

A bangare guda Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci hadin kan kasashen yammaci don tunkarar barazanar Rasha kan Ukraine yana mai cewa matukar Moscow ta iya samun damar yiwa Kyiv mamaya hakan zai zamo firgici ba kadai ga gabashin Turai da Asia ba har da duniya baki daya.

A cewar Boris Johnson yayin jawabinsa a taro kan tsaro na birnin Munich matakan da Rasha ke dauka zai janyo mata takunkuman da za su hana ta damar hada hada a manyan kasuwannin hannayen jari na London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.