Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Rasha na cikin shirin harba makamin nukiliya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci manyan kwamandojin tsaronsa da su sanya jami’an kula da makamin nukiliyar kasar cikin shirin ko ta kwana, bayan ya zargi kasashen Yammacin duniya da daukar matakan nuna kyamar kasarsa.

Shugaba Putin da wasu Hafsoshin tsaronsa
Shugaba Putin da wasu Hafsoshin tsaronsa Sputnik/Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS
Talla

Putin ya ce ya shaida wa Ministan Tsaron kasar da bBbban Hafsa mai kula da rundunonin sojin Rasha da su sanya dakarun da ke kula da makaman nukiliyar cikin shirin yaki.

Shugaban ya shaida wa jama’ar kasar ta kafar talabijin cewar wadannan kasashen Yammacin duniya, bayan nuna kiyayya sun kuma sanya wa kasar h ramcacen takunkumin karya tattalin arziki, yayin da ya zargi manyan kasashen da ke cikin kungiyar NATO da kalamai masu zafi akan kasarsa.

Tuni Ministan Tsaron kasar Shoigu ya amsa umurnin shugaban na sanya dakarun cikin shirin ko ta kwana.

Sai dai kasar Amurka ta zargi shugaban na Rasha da daukar matakan zafafa tashin hankalin saboda umurnin da ya bayar na saka dakarun kula da makaman nukiliyarsa cikin shirin ko ta kwana.

Mai magana da yawun fadar shugaba Jen Psaki ta ce sun saba ganin irin wannan matakin daga shugaban wanda ke kirkirar karya domin biyan bukatun kansa.

Ita ma Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta yi mummunar suka akan wannan mataki wanda ta ce zai dada zafafa rikicin da ke gudana.

Sakataren kKngiyar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana ikrarin shugaba Putin a matsayin rashin hankali musamman ganin abin da yake faruwa yanzu haka a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.