Isa ga babban shafi
Faranshin mai

Farashin mai ya haura dala 140 a kasuwannin duniya

Farashin gangan danyan man fetur ya kara tashi a kwasuwannin duniya, inda ya kai kusan dala 140 a kan kowacce ganga, sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Matatar mai ta Marathon Petroleum Corp 21/04/2020.
Matatar mai ta Marathon Petroleum Corp 21/04/2020. AP - Paul Sancya
Talla

Rahotanni sun ce yau an sayar da man akan Dala 139 da Centi 13 kowanne ganga wanda shine irin sa na farko tun wanda aka gani a shekarar 2008.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ministan kudin Jamus da na harkokin waje ke gargadi akan daukar duk wani mataki na haramta sayen man Rasha.

A ranar Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace suna duba yiwuwar hana Rasha sayar da man ta a kasuwannin duniya, matakin da Jamus wadda ke shugabancin kungiyar G7 ke cewa bam ai dorewa bane, domin kuwa hakan zai hana su samun wutar lantarki a Jamus.

Kasar Jamus na daya daga cikin kasashen da suka dogara da Rasha wajen samun gas da man fetur, inda take sayen kashi 55 na iskar gas daga wurin ta da kuma kashi 42 na man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.