Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Ukraine

Zelensky ya roki Majalisar Amurka ta shiga tsakani a yakinsu da Rasha

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya gabatar da wani roko mai cike da damuwa ga 'yan majalisar dokokin Amurka da su kara tsoma bakin kan yakin da ke wakana a tsakanin kasar sa da Rasha, inda ya dage kan cewa mamayewar da kasar ta yi ta samu nasara, duk da cewa kasashen yamma sun yi kokarin taimakawa Ukraine din da makakamai.

Volodymyr Zelensky yayin jawabinsa ga Majalisar Amurka.
Volodymyr Zelensky yayin jawabinsa ga Majalisar Amurka. AP - Adrian Wyld
Talla

A yayin taron shugaba Zelensky ya nuna hoton faifan bidiyo ga 'yan majalisar dokokin Amurka kan yadda luguden wutar Rasha ya lalata wurare da dama a Ukraine, ko da yake an jiyo shaugaba Vladmir Putin na bayyana cewa ba zai taba bari Ukraine ta zama wani shingen barazana ga kasar sa ba.

Kafin wannan jawabi na shugaba Zelensky ga ‘yan majalisar dokokin Amurka, ya bayyana cewa, sun amince cewa Ukraine ba za ta taba zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO wadda Amurka ke jagoranta ba.

Gabanin Rasha ta kutsa cikin kasar, daya daga cikin manyan bukatun ta dai shi ne kada Ukraine ta kuskura ta shiga kungiyar NATO, kuma ta jima tana cewa babbar bukatarta ita ce kasar  ta kasance cikin 'yan ba ruwanmu a siyasar gabashi da kuma yammacin Turai.

A wani taro ta kafar talibijin da ya jagoranta, Vladmir Putin ya nanata cewa mamayar da kasar sa ta yiwa Ukraine ana samun nasara, kuma lamura na tafiya ne yadda suka tsara tun da fari.

Yanzu haka dai NATO za ta gudanar da wani taron gaggawa a mako mai zuwa a Brussels amma ya zuwa yanzu ta ki amincewa da rokon Zelensky na shiga kai tsaye saboda tsoron fara yakin duniya na uku.

A kaikaice dai, Amurka da sauran kasashen kungiyar tsaro ta NATO na ci gaba da karfafa goyon bayan soji ga kasar Ukraine ciki har da manyan makamai wadanda suka taimaka wajen dakile sojojin Rasha a arewacin Kyiv.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.