Isa ga babban shafi
Yakin Rasha da Ukraine

Hare-haren Rasha sun yi sanadin mutuwar yara 97 a Ukraine - Zelensky

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce yara 97 ne 'yan kasar suka mutu tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki akansu.

Wani karamin yaro cikin daruruwan 'yan gudun hijirar da ke kokarin ficewa daga kasar Ukraine.
Wani karamin yaro cikin daruruwan 'yan gudun hijirar da ke kokarin ficewa daga kasar Ukraine. REUTERS - PAVLO PALAMARCHUK
Talla

Wadannan alkalmuma kuwa sun zo ne a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya ta ce akalla yaro daya ke zama dan gudun hijira duk bayan dakika 1 a Ukraine.

Shugaba Zelensky ya bayyana adadin kananan yaran da suka rasa rayukansu ne a jiya Talata, yayin gabatar da jawabi ta kafar bidiyo ga majalisar dokokin Canada, inda ya kara rokon abokan kawance da su karafafa taimako da goyon bayansu da suke musu.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, yayin gabatar da jawabi ga abokan huldar kasarsa ta kafar bidiyo.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, yayin gabatar da jawabi ga abokan huldar kasarsa ta kafar bidiyo. REUTERS - POOL

Shugaban na Ukraine ya kuma zargi sojojin Rasha da tafka mummunar barna a kasar ta hanyar rusa muhimman gine-gine da suka hada da makarantu, da kuma asibitoci baya ga gidaje.

Canada ta laftawa jami'an Rasha takunkumi

Tuni dai Fira Ministan Canada Justin Trudeau ya sanar da sanya takunkumi kan karin wasu jami'an Rasha 15 da suka hada da manyan mukarabban gwamnati da sojoji wadanda ke da hannu a wannan yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, matakin da a yanzu ya sa adadin mutane da hukumomi na Belarus da Rasha da Canada ta kakabawa takunkumi kaiwa kusan 500.

Rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM ya nuna cewar fiye da mutane miliyan 3 suka tsere daga Ukraine kuma kusan rabinsu kananan yara ne, tun bayan mamayar da Rasha ta soma a karshen watan Fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.