Sojojin Amurka 4 sun mutu a Norway yayin atisayen NATO
Rundunar sojin Scandinavia ta sanar cewa wani jirgin sojin Amurka da ke atisaye cikin kungiyar tsaro ta NATO ya yi hatsari a kasar Norway, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dukkan sojojin Amurka hudu da ke cikinsa.
Wallafawa ranar:
Mutanen hudu dai na halartar atisayen sojan da ake yi na Cold Response wanda ya kunshi dakaru 30,000 daga kungiyar tsaro ta NATO da kuma kasashen kawance.
Kimanin jirage 200 da wasu jiragen ruwa 50 ne ke halartar atisayen, wanda za a ci gaba da gudanar shi har zuwa ranar 1 ga watan Afrilu.
Tun a yammacin ranar Jumma’a aka bada rahoton bacewar jirgin samfurin V-22B Osprey na rundunar sojojin ruwan Amurka a kudancin Bodo da ke arewacin Norway.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu