Isa ga babban shafi
Afrika-Yunwa

Manyan kasashe sun taimaka da kusan dala biliyan 2 don magance yunwa a Sahel

A kokarin da ake yi wajen magance karanci abinci a yankin Sahel, hukumar kula da abinci da harkokin noma ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kasashen duniya sun bada gudunmuwar dala miliyan dubu daya da miliyan dari tara da 50 don saukaka matsalar yunwar da ake fuskanta a yankin Sahel da tafkin Chadi a wannan shekarar.

Yunwa na ci gaba da tsananta tsakanin kasashen yankin Sahel.
Yunwa na ci gaba da tsananta tsakanin kasashen yankin Sahel. AP
Talla

An dai bude gidauniyar ce a lokacin wani taro wanda gamayyar kasashen yankin Sahel da na yammacin Afrika da kungiyar tarayyar Turai da kuma cibiyar da ke yaki da karancin abinci ta kasa da kasa suka shirya.

A cikin wata sanarwar da hukumar kula da abinci da harkokin noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce, gudunmuwar da kungiyar Tarayyar Turai ta bayar shi ne mafi girma, inda ta sanya Euro miliyan 240 kari kan Euro miliyan 654 da a baya ta alkawaran ta bayarwa a matsayin gudunmuwa.

Faransa na daga cikin wadanda suka bada gudunmuwa mai gwabi ta Euro miliyan 166 a wannan shekarar don samar da abinci.

A cewar alkaluman da hukumar ta fitar, karancin abinci a yankin ya karu tun daga shekarar 2019, inda ya shafi kusan mutum miliyan 40 idan aka kwatanta da na shekaru 3 da ya shafi mutum miliyan 10 da dubu dari 8 kawai.

Matsanancin fari da annobar cutar corona da kuma rikicin Ukraine da Rasha na daga cikin ababen da ke kara matsalar karancin abincin da ake fuskan ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.