Isa ga babban shafi
RASHA-UKRAINE

Rikicin Rasha da Ukraine na ci gaba da jefa duniya cikin wani yanayi - MDD

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce rikicin Rasha da Ukraine na ci gaba jefa duniya cikin yanayi na rashin tabbas, sakamakon hauhawar farashin abinci da kuma na makamashi a sassan duniya. Guterres wanda ke jawabi lokacin da yake karbar wani rahoto da kwararrun Majalisar suka gabatar dangane da tasirin wannan yaki.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin zantawa da magana da manema labarai game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Amurka, Maris 14, 2022.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin zantawa da magana da manema labarai game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Amurka, Maris 14, 2022. REUTERS - ANDREW KELLY
Talla

Antonio Guterres yace, wannan yaki ya yi matuakar tasiiri ga kasashen duniya, inda kawo yanzu illolinsa suka shafi akalla mutane biliyan daya da milyan 700 a sassan duniya.

Guterres yace, da dama daga cikin wadannan mutane na rayuwa ne a cikin matsanancin talauci, sun samu kansu a yanayi na rashin abinci da makamashi sannan ga karanci kudi a hannayensu. Wannan na nufin cewa mafi yawansu na fuskantar matsanancin talauci da kuma yunwa.

Yanzu haka kasashe 36 na duniya sun dogara ne da Rasha da Ukirane don sayo rabin alkamar da suke amfani da ita a kowace rana. Wannan yaki ne da ya haddasa tashin farashin alkama da akalla kashi 36.

Kamar yadda aka sani, Rasha na matsayin daya daga cikin kasashen da ke samar wa duniya da makamashi, saboda haka farashin mai ya karu da kusan 60% a cikin shekara daya, wannan ya wuce tunanin manazarta, inji Guterres.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.