Isa ga babban shafi
Rasha - uKRAINE

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da Rasha daga hukumar kare hakkin dan adam

Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar dakatar da Rasha a matsayin mamba a Hukumar Kare Hakkin Bil’adma ta Majalisar sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Allon dake nuna sakamakon ƙuri'a kan dakatar da Rasha daga Hukumar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a yayin wani taron gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Amurka, 7 ga watan Afrilu 2022.
Allon dake nuna sakamakon ƙuri'a kan dakatar da Rasha daga Hukumar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a yayin wani taron gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Amurka, 7 ga watan Afrilu 2022. REUTERS - ANDREW KELLY
Talla

Daga cikin kasashe 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya, 93 sun kada kuri’ar amincewa da dakatar da Rasha kamar yadda Amurka ta bukata, yayin da kasashe 24 suka ki amincewa da matakin, 58 kuma suka yi rowar kuri’arsu.

Kuri’ar ta nuna karara yadda kawunan kasashen duniya suka rarrabu dangane da ladabtar da Rasha kan hare-harenta a  Ukraine.

Kasa ta biyu

A karo na biyu kenan a tarihi da ake dakatar da wata kasa a Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, inda aka fara daukar makamancin wannan mataki kan Libya a shekara ta 2011.

Dokar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, dole ne a samu kashi biyu bisa uku na mambobin da suka amince kafin dakatarwar ta tabbata, amma banda kidayar kasashen da suka yi rowar kuri’arsu.

China ta yi goyi bayan Rasha

Kasashen da suka ki goyon bayan dakatar da Rasha sun hada da China wadda ke zama aminiya sosai ga Moscow, sai kuma Iran da Kazakhstan da Cuba da Belarus da  Syria.

Afirka sun yi rowar kuri'u

Da dama daga cikin kasashen Afrika sun kaurace wa zaman kada kuri’ar duk da matsin lamnbar da Rasha ta yi musu, kamar Afrika ta Kudu da Senegal.

Su ma kasashen Brazil da Mexico da India sun yi rowar kuri’arsu.

Amurka ta bayyana matakin dakatarwa a matsayin ladabtarwa ga Rasha saboda harin da ta fara kaddamarwa a Ukriane tun a ranar 24 ga watan Fabairun da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.