Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu-MDD

Ramaphosa ya caccaki salon kamun ludayin MDD kan rikicin Rasha da Ukraine

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da ke shan suka kan kin yin tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ya caccaki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da cewa ya na bukatar garambawul don tafiya dai dai da zamanin da ake.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu. AFP - THEMBA HADEBE
Talla

Shugaban Cyril Ramaphosa ya ce rikici tsakanin Rasha da Ukraine ya fallasa gazawar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke da shi wajen gudanar da ayyukansa don tabbatar da zaman lafiya a sassan Duniya.

A cewar shugaban wanda har zuwa yanzu kasar sa ta ki yin tir da Rasha haka zalika ta kauracewa kada kuri'a a kudurorin majalisar 2 da aka amince da su kan Ukraine, ya zargi mahukuntan kasashe da zamowa 'yan amshin shata, yana mai cewa babu hadin kai a lamurran tabbatar da zaman lafiya ga sassan duniya daga zauren Majalisar.

Ramaphosa wanda ke bayyana hakan ga manema labarai a birnin Pretoria, ya ce tsarin na Majalisar Dinkin Duniya ya bai wa kasashe masu karfi damar yin amfani da karfinsu wajen yanke shawarwarin da a wasu lokuta su ke da hadari, lamarin da a cewarsa irin wadannan tsare-tsare sun tsufa da halin da duniya ke ciki a yanzu.

Shugaban na Afrika ta kudu kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, ya ce akwai bukatar dawo da tsarin Demokradiyya a zauren Majalisar ta yadda majalisar za ta kasance mai gaskiya ga aikinta da kuma kaucewa wuce gona da iri da wasu tsirarun kasashe ke yi.

Wannan kalamai na Ramaphosa na zuwa ne a dai dai lokacin da a yau Alhamis Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'ar da ta dakatar da Rasha daga kasancewa mamba a kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar sakamakon abin da ta ke aikatawa a Ukraine, hukuncin da ke biyo bayan bukatar hakan daga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.